اذا لم تجد ما تبحث عنه يمكنك استخدام كلمات أكثر دقة.
GABATARWA
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinƙai.
Salati ya tabbata ga shugabanmu jagoranmu abin so da koyi, Muhammad (S.A.W) da iyalansa, da sahabbansa baki ɗaya.
Bayan haka:
Tare da ƙarancin shekaruna da ba za su gaza shatara (19) ba, na yi tunanin na fassara wannan littafi a wancan lokaci don sauƙaƙa wa ɗaliban makarantarmu fahimtar abin da ya ƙunsa, bayan yawaita koke a kan wahalar da yake ba su wajen fassarar ibarorinsa, musamman cikin mas’alolin da ya ambata, hakan ya faru ne gare ni sakamakon koyarwa da aka nemi na fara a makarantar, bayan kammala saukar karatun Alƙur’ani mai girma.
Na fara wannan aikin tun ban kammala littafin a gaban malami ba, inda muke karantar sa a gun malaminmu sheikh Yakub Musa Yakub Sautus Sunnah, duk da an yi babi biyu na farko babu ni, wanda na koye su a gun malam Rayyanu Sulaiman lokacin da muke koyarwa a tahfiz ta makarantar Irshadul Aulad Islamiyya ‘Yar Kwajalawa Zangon Dakata Kano. Bayan nan na fa’idantu da sauraren karatun sheikh Ja’afar Mahmud Adam Allah Ya yi masa rahama.
Daga cikin littattafan da na yi amfani da su akwai:
Fat’hul Majid na Abdurrahman bin Hassan bin Muhammad bin Abdulwahab jikan mai littafin.
Taisirul Azizil Hamid na sulaiman bin Abdullahi bin Muhammad bin Abdulwahab jikan mai littafin.
Ƙaulul Nufid na Usaimin. Da sauransu.
JAWABIN GODIYA
Ba zan manta da waɗanda suka ba ni gudummawa ba wajen ganin an buga wannan littafi, musamman waɗanda suka ɗauki ragamar ganin an ya ɗa shi don al’umma su amfana, bayan kammala karatun sa a manhajar Tiktok, gidan malama ‘Yar Borno Sunnah Sak (Salamatu Ilyasu Zakariyya).
Ga sunan kamar haka:
Dr. AHMAD MU’AZ (Ahmerdb)
ENGR. JAZULI ALKASIM (J.A ZANGO)
ASHIRU ABDULLAHI (Addausawy1)
ABDULHAKIM (JAJAWY)
SALAMATU ILYASU ZAKARIYYA (‘YAR BORNO SUNNAH SAK)
HABIBA (MAMAN BABY)
Muna fatan Allah Ya yi musu sakayya da gidan Aljanna amin.
Almajirin ilimi:
ISMA’IL ABDULLAHI IS’HAƘ
Isma’el Ibn Katheer
09028287628
01/02/2025
TARIHIN MAWALLAFI
SHEIKH MUHAMMAD BIN ABDULWAHAB
Shi ne Muhammad bin Abdulwahab bin Sulaiman bin Ali bin Muhammad bin Ahmad bin Rashid bin Mushrif At-Tamimi An-Najdi Al-Hambali.
An haife shi a garin Uyaina da ke yamma da birnin Riyad a sheikhara ta 1115 bayan Hijira.
Ya fara ɗaukar ilimi daga babansa Abdulwahab bin Sulaiman, ya fara karantar Fiƙihu, da Tafsiri, da Hadisi, da kuma maganganun manyan malamai dangane da Musulunci. Ya kasance mai ƙoƙari da saurin fahimta ,da saurin hadda, kuma ya haddace Ƙur’ani kafin ya cika sheikhara goma.
Ya ci gaba da neman ilimi a cikin birnin Madina a gurin Sheikh Abdullahi bin Ibrahim bin Saif Annajadi da Sheikh Muhammad Hayat Assundi Almadnii, sannan ya tafi i zuwa garin Basra (Iraƙi) inda ya karanci Fiƙihu da Lugha daga malamai masu yawa kamar Ash-sheikh Muhammad Al-Majmu’i.
Ya samu saɓani da mutanen Basara a kan abin da suke aikatawa na bidi’a da shirka, saboda haka ne ya sa mutane suka fara yunƙurin cutar da shi, har sai da suka fitar da shi daga garin.
Ya dawo garin Harimla’a 1139 bayan Hijra, ya tattauna da mahaifinsa a kan abubuwan da wasu jahilan mutane suke aikatawa na bidi’a da kuma shirka. Mahaifinsa ya rasu a sheikharar 1153 bayan Hijira.
Muhammad bin Abdulwahab ya ci gaba da yaɗa da’awa da kuma umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna, saboda haka ne wasu daga cikin gurɓatattun mutane suka shirya yadda za su kashe shi, sai dai kuma ba su yi nasara ba.
A dalilin wannan abu da mutane suka yi masa sai ya dawo gida, sarkin Uyaina na wannan lokacin shi ne Usman bin Mu’ammar, kuma ya yi maraba da zuwansa, kuma ya karrama shi.
Ya yi aure a Uyaina shi da Jauharatu binti Abdullah ibin Mu’ammar.
Ya yi kiran Sarkin Uyaina i zuwa Tauhidi kuma ya amsa ya kuma taimaka masa wajen yaɗa da’awa.
Ya ci gaba da yaɗa da’awa, yayin da ya raba da’awar tasa gida uku:
I zuwa ga sarakuna
I zuwa ga malamai
I zuwa ga sauran mutane
Kiran da ya dinga yi wa malamai ya yi amfani da salon tura musu wasiƙu, waɗanda suke kusa da garinsa kuma yana zuwa ne ya same su har gida, wasu sun amsa masa wasu kuma ba su amsa ba, wannan ya sa suka dinga haɗa shi da masu mulki.
Da yawan sarakuna ba su amsa masa ba kamar irin su Sulaiman bin Muhammad bin Garir Alhumaidi.
Dalilin haka ne ya sa ya yi ƙaura zuwa garin Sarki Muhammad bin Sa’ad, ya sauka a gidan wani mutum mai suna Muhammad bin Suwailim, wanda shi kansa mutumin yana tsoron hukuncin sarki idan ya gane a gidansa ya sauka.
Bayan saukarsa a wannan gida ɗalibansa suka dinga ziyartar sa daga sassan ƙasashe da garuruwa, a cikin ɗaliban akwai waɗanda suke da kusanci da matar sarki wato Maudi bintu Wadban, ta kasance mai hankali da tunani, sun yi mata bayani a kan gaskiyar abin da Muhammad bin Abdulwahab yake da’awa a kansa, saɓanin yadda mutane suke yaɗa jita-jita cewa ba ya son Annabi, ba ya son Waliyai, inda ita kuma ta sanar da mijinta cewa haƙiƙa wannan mutumin ganima ce Allah Ya ba ka, don haka ka karrama shi, ka girmama shi, domin ka ci moriyar abin da ya zo da shi, sai ya yarda da haka, kuma Allah Ya sanya masa soyayyar Muhammad bin Abdulwahab.
Muhammad bin Sa’ad ya je gurin Sheikh Muhammad bin Abdulwahab a gidan da ya sauka ya ce da shi: “Ina yi maka barka da zuwa garin da ya fi maka alheri a kan garinka, sannan ina yi maka bushara da samun zaman lafiya da kuma girmamawa.” Bayan haka sheikh Muhammad ya yi masa bayani a kan da’awar da yake yi zuwa kaɗaita Allah (Tauhidi)
Muhammad bin Sa’ad da Sheikh Muhammad bin Abdulwahab sun ci gaba da samun nasarori ta hanyar hujjojin da sheikh Muhammad yake da su na Ƙur’ani da Hadisi da kuma kaifin takobin Muhammad bin Sa’ad.
Sheikh Muhammad ya ci gaba da karantarwa ga dalibansa da suke zuwa daga ko’ina a faɗin duniya, sannan ya ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali a wannan gari saboda tsaron da yake da shi na sojoji. A wannan gaɓar ne nake so na yi wa ‘yan’uwa bayani a kan wasu shubuhohi da ake yaɗawa a kan da’awarsa, dangane da abin da ɗan’uwansa sheikh Sulaiman ya rubuta a wata risala da maƙiyan da’awar suka sanya wa suna da: “ASSAWA’IƘUL ILAHIYYA FIR RADDI ALAL WAHHABIYYA” saboda ƙiyayya da sharri.
Yadda abin ya faru shi ne, a farkon lamari Sulaiman ya yi wa ɗan’uwansa raddi a kan da’awar da yake yi, har ya soke shi da wasu maganganu masu nauyi bisa son zuciya, amma daga baya ya nemi yafiyarsa kuma ya sauka daga abin da yake kai na bid’a da ɓata ya tuba ya bi da’awar yayansa Muhammad bin Abdulwahab.
Allah ya yi wa Sheikh Muhammad bin Abdulwahab rasuwa ranar Litinin a ƙarshen watan Shawwal na Shekarar 1296 bayan Hijira, ya rasu yana da shekara 92.
Ya kasance mutum ne mai ijtihadi da kuma hukunci na gaskiya, sannan mai tausasa wa na kusa da shi, bai bar wani abu na dukiya ba wanda magada za su gada, sai dai ya bar masu bashi mai yawa.
Mafi shaharar tittattafansa su ne:
Kitabut-Tauhid
Kashfush-Shubuhat
Usulus-Salasa
Mukhtasarus-Sira
Nasihatul-Muslimin
Kitabul-Kaba’ir
Usulul-Iman
Masa’ilul-Jahiliyya
Mukhtasaru Zadul Ma’ad
Ahadisul Fitan
Da kuma sauransu waɗanda yawa-yawansu ya wallafa su ne a kan Tauhidi.