English  

كتب tsarabar ya mace zuwa gidan mijinta

اذا لم تجد ما تبحث عنه يمكنك استخدام كلمات أكثر دقة.

عرض المزيد

Tsarabar 'Ya Mace Zuwa Gidan Mijinta (كتاب)


Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, kuma tsira da amincin Allah su tabbata bisa ga shugabanmu Annabi Muhammad ﷺ, da alayensa, da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu da gaskiya da kyautatawa har izuwa ranar sakamako.

Bayan haka; A cikin zamantakewar aure mai tsarki, mu na da bakutuwa izuwa ga nasihohi domin fuskantar jarabtu da kalubalen rayuwa tare da abokan rayuwar mu. Wannan tarin nasihohi guda hamsin, an tsara su ne bisa ƙauna da kulawa, daga mahangar addinin Musulunci, musamman ga yan’uwa matan aure Musulmai masu burin gina zamantakewa mai cike da zaman lafiya da takawa.

‘Yar uwa Musulma mai daraja, aure ba wai haduwar mutane biyu kawai ba ne; wata alâka ce mai tsarki wadda ta samo asali daga girmama juna, ƙauna da bin koyarwar Musulunci.

Nasihohin da aka gabatar anan na nufin inganta ginshikin zamantakewarku, ƙarfafa fahimtar juna tsakaninku, da kuma gina gida mai cike da ƙauna, soyayya, jinkai, hakuri da juna, natsuwa, tarbiyya, tare da tsoron Allah.

Yayin da nake nazarin halin da auren zamani ke ciki, na rubuta wannan da fatan cewa zai haskaka miki hanya, ya saukake miki tafiya, ya gyara zamantakewarku, kuma ya zama tushen farin ciki gare ku. Allah Ya albarkaci aurenku, Ya ba ki juriya, kuma Ya cika rayuwarku da kwanciyar hankali, ƙauna, da duk natsuwa.

Ina roƙon Allah, Mai Girma da daukaka, Ya karɓi wannan hidima daga gare ni, Ya amfanar da al’ummarmu, kuma Ya sanya shi a matsayin hanya ta shiryar da mutane zuwa ga imani, biyayya gare Shi, da bin tafarkin Ma’aikinsa, Annabi ﷺ.