English  

كتب interfaith lauje ne cikin nadi

اذا لم تجد ما تبحث عنه يمكنك استخدام كلمات أكثر دقة.

عرض المزيد

Interfaith Lauje ne cikin nadi (كتاب)


Ma’anar‘Interfaith’
‘Interfaith’: kalma ce ta Turanci da ‘Oxford Dictionary’ ya bayyana ta da cewa ‘Between or connected
with people of different religion’. Wato ‘tsakanin kodangane da mabiya addinai mabambanta’. Wannan
ya na nuni da cewa Kalmar ta ‘Interfaith,’ sifa ce (wato adjective) wacce sai an danganta ta da wata
kalmar (watosuna (noun a Turance) kafin ta ba da cikikkiyar ma’ana, a maf iyawancin lokuta. Misali a ce:
‘Interfaith dialogue/discourse/movement/relations… ‘.
Bisa yanayin yanda a ke mu’amalantar wannan kalma ta ‘Interfaith’ ta fuskar aiwatarwa, za mu iya cewa
ta nada ma’anoni guda biyu – zahira da baɗina, wato ma'ana ta fili da ta ɓoye. Ma’ana ta filin kyakkyawa
ce wadda ita ake bayyana wa mutane don a fisgi hankulansu da ita, amma dai ba ita ce manufar ba.
Ma’ana ta ɓoye kuwa ba a bayyana wa mutane domin mummna ce ga shi kuwa ita ce manufar. Wato dai
mafiya wancin lokuta masu yaɗa manufofin ‘interfaith’ su na da ɓoyyayiyar manufa ta dasisa domin
cimma burinsu na dilmiyar da al’ummah. Babbar manufar kuwa it ace aiwatar da ‘syncretism’, wato
dunƙule addinai, domin a kawar wa masu imani imaninsu.
Kalma ce da ma’anar ta ke da ruɗani, wanda hakan ya haifar da saɓanin fahimtar jama’u har ma da
Mallamai game da ita; inda wasu ke ganin cewa abu ne mummuna wasu kuwa ke ganin akasin haka.
A zahirin gaskiya dai fakewa a ke da guzuma a harbi karsana wajen aiwatar da manufofin ‘interfaith’. Za
mu fi fahimtar haka idan muka dubi irin zaƙewar da Yahudawa da Nasara ke yi a kan cimma manufofin
’interfaith’. Allah Ta'ala kuwa Ya bayyana mana burinsu a kan mu, inda Ya ke cewa:

وَدُّوا لَوْ تَكْفُرُونَ كَمَا كَفَرُوا فَتَكُونُونَ سَوَاءً ۖ فَلَا تَتَّخِذُوا مِنْهُمْ أَوْلِيَاءَ حَتَّىٰ يُهَاجِرُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ ۚ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَخُذُوهُمْ وَاقْتُلُوهُمْ حَيْثُ وَجَدْتُمُوهُمْ ۖ وَلَا تَتَّخِذُوا (النّساء 89:4) : المختصر في تفسيركما