اذا لم تجد ما تبحث عنه يمكنك استخدام كلمات أكثر دقة.
Wannan Littafin kamar yadda muka gani littafi ne na babban malamin mu Allah ya saka masa da Aljanna, wato Sheikh Muhammed Salih AAl-Munajji, wanda ya rubuta shi akan abubuwan da aka hana a musulunci acikin dukkan nauikan ibada, malam ya yi kokarin rubuta littafin akan tsari na babi babi (wato duk mas'ala sai ya yi mata babi sai ya kawo abubuwan da aka haramta acikin ta) kamar yadda muka sani, addinin musulunci addini ne mai sauqi da dadi musamman ga wanda ya fahimce shi, kuma Allah ya sanya sauqi acikinsa ta hanyar halatta abubuwa da dama ga bayi da basu sauƙi acikin su, kamar inda Allah ya gayamana cewa: "Allah ba Ya nufi domin Ya sanya wani ƙunci a kanku" suratut taubah ayata 6. Kuma shiyasa malamai suka ce, abubuwan da shari'a ta haramta ba su da yawa, iya abin da aka ambata cewa haram ne su ne haramun, amma duk abin da shari'a ta zo bata ce komai akan sa ba wannan abun baya zaman haramun sai dai idan an samu wani nassi, ko ijma'in malamai, ko qiyasi dss da suke nuni abun yana kai wa zuwa ga haram, amma dai asali halal ne, kamar shan lemon kwalba, cin naman tattabara, dss.